🎓 HRH Emir of Dukku Donates ₦100,000 to NADS Dukku Chapter for Student Enlightenment Program
Mai Martaba Sarkin Dukku, Alhaji Haruna Abdulkadiri Rashid II, CON, ya bai wa Kungiyar Daliban Dukku (NADS) reshen Dukku gudummawar naira dubu ɗari (₦100,000) domin tallafawa shirin wayar da kai ga Daliban Firamare da Sakandare da kungiyar ke shirin gudanarwa a zangon karatu na biyu da za a bude mako mai kamawa.
“Ilimi ginshiki ne na ci gaban kowace al’umma. Ya kamata yara su fara fahimtar muhimmancin karatu tun suna ƙanana,” in ji Sarkin Dukku.
Shugabannin NADS sun nuna godiya matuƙa bisa wannan kyakkyawan goyon baya, inda suka ce gudummawar za ta ƙarfafa su wajen kai sakon ilimi zuwa makarantun yankin.

Ana sa ran shirin zai kunshi jawaban ƙarfafa gwiwa, shawarwari daga malamai da kwararru, da tattaunawa da dalibai a makarantu da dama a cikin ƙaramar hukumar Dukku.
✅ Masarautar Dukku na alfahari da cigaban ilimi a tsakanin matasa kuma tana maraba da duk wata gudunmawa da ke ƙarfafa karatu da basira.